Home Labaru Boko Haram: Jami’an Soji 3 Sun Rasa Ransu A Arangama Da ‘Yan...

Boko Haram: Jami’an Soji 3 Sun Rasa Ransu A Arangama Da ‘Yan Ta’adda A Borno

815
0

Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’anta ukku sun rasa rayukansu, yayin da wasu 8 suka jikkata a musayar wuta da suka yi da ‘yan ta’addan Boko Haram a Munguno dake jihar Borno. 

Colonel Sagir Musa

Mai rikon mukamin daraktan yada labarai na rundunar Colonel Sagir Musa ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce har ila yau jami’an sojin na rundunar Operation Lafiya Dole sun kashe ‘yan ta’addan na Boko Haram da dama yayin da wasu kuma suka tsere da raunin bindiga a jikinsu.

A nata banagen rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce jami’anta dake aiki karkashin Operation Lafiya dole sun sun lalata sansanonin ‘yan ta’addan, tare da kashe ‘yan Boko Haram da dama ta harin sama da ta kai.

Jami’in yada labarai na rundunar Air Commodore Ibikunle Daranola, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa.