Home Labaru Ingancin Irin Shuka: Ministan Harkokin Noman Najeriya Ya Koka

Ingancin Irin Shuka: Ministan Harkokin Noman Najeriya Ya Koka

747
0

Ministan kula da harkokin noma, Sabo Nanono ya ce jamhuriyar Nijar ta fi Najeriya mallakar ingantaccen irin shuka duk da yadda Nijar din ke da yankin hamada mai fadi.

Nanono wanda ya fara aiki ba da dadewa ba, na wannan bayanin ne a wani taron hukumar bunkasa ingantaccen iri ta Najeriya da aka yi.

Ministan ya nuna damuwa kan cewa akwai hukumomin bincike da masana kan lamuran noma amma labari kawai a ke yi ba a samar da iri mai inganci da zai kai harkokin noma gaba kamar yadda Indiya ta yi nasarar zama mai nomawa da fitar da alkama kasashen ketare.

Haka kuma, Nanono ya nuna damuwa akan yadda ba a maida hankali akan iccen gawo wanda bayan samar da taki, ya kan taimaka wajen yaki da hamada.

Ministan ya kuma ce a Nijar ko dan gidan Firai minista bai isa ya sare iccen gawo ba, amma ga shi nan ‘yan Nijar su na shigowa Najeriya su na kada iccen.