Home Labaru Rohoton Rashawa: Najeriya Ta Yi Wa Kungiyar Transparency Raddi

Rohoton Rashawa: Najeriya Ta Yi Wa Kungiyar Transparency Raddi

329
0
Rohoton Rashawa: Najeriya Ta Yi Wa Kungiyar Transparency Raddi
Rohoton Rashawa: Najeriya Ta Yi Wa Kungiyar Transparency Raddi

Gwamnatin tarayya ta maida martani kan rahoton kungiyar hana cin hanci da rashawa ta duniya wato Transparency International da ya bayyana Najeriya a matsayin kasar dake kan gaba wajen fama da matsalar cin hanci da rashawa a yammacin nahiyar Afrika, binciken da gwamnatin ta bayyana a matsayin mara tushe ballantana makama.

Ranar Alhamis 23 ga Janairun 2020, kungiyar Transparency International ta fitar da rahoton da ta saba fitarwa duk shekara kan matsayin kasashe da kokarin yakar cin hanci da rashawa.

A rahoton har’ila yau kungiyar ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 34 a duniya wajen fama da wannan matsala, kazalika kasa ta 146 cikin 180 a fagen kokarin magance matsalar ta cin hanci ko rashawa, bayan da ta samu maki 26 cikin 100 a 2019, sabanin maki 27 a shekarar 2018.

Wasu daga cikin dalilan da Transparency International ta zayyana a matsayin ginshikan binciken ta kan Najeriya sun hada da, rashin adalci wajen hukunta wadanda aka samu da laifukan cin hanci da rashawa ta hanyar kauda idanu kan wani bangare, musamman masu mulki da kuma attaijirai.

kungiyar ta ce wasu abubuwan dake haddasawa yakar cin hanci da rashawa a Najeriya cikas, su ne rashin kyakkyawar alaka tsakanin wasu kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula, da rashin kyakkyawar fahimta kan matsalar ta cin hanci da hanyoyin magance ta, da kuma kazantar matsalar  a muhimman bangarori da suka hada da tsaro, da kuma man fetur da iskar gas.

To sai dai Ministan Shari’ar Najeriya Abubakar Malami, da hukumar hana zambarkudi da karya tattalin arzikin kasa EFCC sun yi Allah-wadai tare da yin watsi da rahoton. wanda suka bayyana a matsayin bita da kulli.