Kungiyar da ke tsaya wa mata su rika sanya guntun Siket mai suna ‘Serve With Skirts Movement’, ta gudanar da zanga-zangar lumana tare da kira ga hukumar kula da dalibai masu aikin bautar kasa ta amince wa mata su rika sa gajerun siket a lokacin aikin yi wa kasa hidima.
Shugabar kungiyar Udochi Emmanuel, ta ce duk shekara sai ma’aikata ko sojojin da ke sansanin NYSC sun tozarta mace a kan rashin sa wando a sansanin.
Udochi ta cigaba da cewa, hakan da ake yi bai kamata ba, saboda tauye masu hakki ne ake yi kamar yadda dokar kasa ta gindaya.
Ta ce sun yi ta bibiya da kira ga hukumar NYSC, ta amince wa duk dalibar da ba ta son sanya wando ta rika sanya siket, amma hukumar ta toshe kunnuwan ta.
Kungiyar ta gudanar da zanga-zanga ne, bayan hukumar NYSC a jihar Ebonyi ta kori wasu mata biyu daga sansanin horo saboda rashin sanya wando.
You must log in to post a comment.