Kotu ta saki mutumin da ya soka wa shugaban kasar brazil Bolsonaro wuka a lokacin yakin neman zabe a watan Satumba na shekara ta 2018, bayan wani alkali ya yanke hukuncin cewa mutumin ya na da tabin hankali.
Ba za a iya yi wa Adélio Bispo shari’ah a karkashin dokokin Brazil ba, saboda ba ya da cikakkiyar masaniya a kan abubuwan da ya aikata a lokacin kamar yadda alkalin ya yanke hukunci.
Sai dai ya ce mutumin ya na da matukar hatsari, don haka ya daure shi tsawon wani lokaci maras iyaka ta yadda zai samu kulawar likitoci.
Sai dai Shugaba Bolsonaro ya ce zai yi kokarin ganin an soke hukunci bayan ya gana da lauyan sa.
Shugaban, wanda sai da aka yi ma shi aiki bayan faruwar lamarin, ya nuna cewa siyasa ce ta sa aka kai masa harin, kuma wasu mutane ne su ka kitsa lamarin ba kawai Mista de Oliveira ba.