Shugaban Al’ummar Arewa mazauna kudancin Najeriya Alhaji Musa Saidu ya kalubalanci kungiyar wanzar da zaman lafiya ta matasan Arewa da suka yi zargin cewar Chief Edwin Clark na daga cikin mutanen da ke rura wutar rikicin siyasar jihar Ribas.
Musa Saidu ya bayyana hakan ne a’ yayi da yake hira da kamfanin dillacin labarun Najeriya wato NAN a birnin Fatakwal ta jihar Ribas, inda ya kara da cewar Chief Edwin Clark Dattijo ne mai mutunci da kishin kasa, inda ya kara da cewar shi Chief Harold Dappa-Biriye sune suka yi fafutukar ganin an kafa Hukumar raya yankin Neja -Delta ta NDDC
Ya ce ya Kadu kwarai da gaske da ganin labarin a wata jarida duk da yake shugabannin kungiyar ba su saka sunayensu a ciki ba wadda hakan ke nuni da cewa kungiyar babu ita kwata kwata a zahirance,wata kila wasu ne ke daukar dauyin irin wannan rubutun batanci ga Chief Edwin Clark, wanda kuma yana da kyakkawar amintaka da Arewa
Ya kara da cewa lokacin da aka kafa kungiyar Tuntuba ta Arewa wato ACF sai da ta kulla dangantakar hadaka da kungiyar Al’ummar Kudu maso Kudu wato SSPC a ranar 17ga watan Nuwamba na shekara ta 2000, kuma ko lokacin jamhuriya ta farko akwai kyakkawar alaka tsakanin sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da marigayi Chief Harold Dappa-Biriye.














































