Home Labarai Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ce Adadin Mutanen da Suka Mutu a’ Maiduguri ta Kai...

Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ce Adadin Mutanen da Suka Mutu a’ Maiduguri ta Kai 30

256
0
download (4)
download (4)

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta fara tattara alƙaluman mutanen da aka rasa a ibtila’in ambaliyar ruwan da ta afkawa birnin Maiduguri a jihar Borno.

Mahukuntan jihar sun ce zuwa yanzu an tattara gawar mutum 30 yayinda NEMA ke ci gaba da aikin laluben waɗanda suka maƙale a saman rufin gidaje da wurare masu haɗari.

Hukumar NEMA ta ce ambaliyar ta shafi mutum miliyan 1 da rabi waɗanda ke halin tsananin buƙatar agaji, musamman ganin yadda suka bar muhallan su a yanayi na ɗimuwa sakamakon mummunar ambaliyar wadda ta faro da tsakaddaren Talata.

Mai magana da yawun hukumar ta NEMA Ezekiel Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kawo yanzu mutum 30 suka tabbatar da mutuwar su ko da ya ke alƙaluman ka iya ƙaruwa sakamakon yadda har yanzu aka gaza gano mutane da dama da suka bace a ruwan.

Tun farko ɓallewar madatsar ruwa ta Alau, ita ta haddasa tumbatsar ruwa a tituna da magudanan ruwan Maiduguri wanda zuwa yanzu ya lalata tarin kadarorin da ba a kai ga ƙiyasin ƙudin su ba, baya ga gine-gine da gidajen jama’a da kuma wuraren kasuwanci.

Leave a Reply