Home Labaru Rikicin Siyasa: Lamurran APC Su Na Ba Ni Tsoro Da Mamaki –...

Rikicin Siyasa: Lamurran APC Su Na Ba Ni Tsoro Da Mamaki – Okorocha

228
0
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo

Tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana takaicin sa game da yadda jam’iyyar APC ta maida shi abokin gaba duk da irin bautar da ya yi mata tun daga shekara ta 2015.

Ya ce wai a yau shi ne abokin gabar jam’iyyar APC a Nijeriya, duk da irin bautar da ya yi mata da irin tallata ta da ya yi a yankin Kudu Maso Gabas, amma duk da haka shugabannin ta sun kafa ma shi kahon zuka.

Okorocha ya kara da cewa, a yankin Kudu Maso Gabas har kiran sa ake yi da ‘Inyamirin Hausawa’, amma duk da haka cin mutuncin yau dabam da na gobe ake yi ma shi a jam’iyyar APC.

Ya ce abin da jam’iyyar APC ta ke yi ma shi ya tada ma shi da hankali kuma ya na ba shi tsoro, ya na mai cewa, yanzu bai san matsayin sa game da dakatarwar da dajam’iyyar APC ta yi ma shi ba.

Rochas ya cigaba da cewa,  a halin yaznu shugaba Buhari ne karfin jam’iyyar, amma idan ya kammala wa’adin sa ya na tabbatar da cewa komai zai sauya saboda babu hadin kai a jam’iyyar.