Home Labaru Harin Gudumbali: Boko Haram Ta Kashe Sojojin Nijeriya Da Dama

Harin Gudumbali: Boko Haram Ta Kashe Sojojin Nijeriya Da Dama

1431
0

Majiyoyin tsaro a Nijeriya, sun ce sojoji da dama sun rasa rayukan su, sakamakon harin kwanton-bauna da mayakan Boko Haram su ka kai kusa da garin Gudumbali da ke jihar Borno a ranar litinin da ta gabata.

Harin dai ya na zuwa ne, bayan sojojin ke kan hanyar su ta kai dauki ga wasu sojojin Nijeriya da na Chadi da ke kokarin kwace garin Gudumbali daga ‘yan Boko Haram, inda mayakan su ka yi amfani da mayan makamai ciki har da rokoki a kan su.

Shaidu sun ce an kashe gwamman sojoji tare da lalata motoci da makaman su.

Wannan harin dai ya na kara nuna yadda ‘yan Boko Haram ke ci-gaba da zama babbar barrazana ga gwamnatin Nijeriya.