Rundunar yan sandan jihar Kano ta haramta duk wani gangami ko taron jama’a a jihar har sai baba-ya-gani.
Umurnin na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna, wanda aka ba manema labarai a Kano.
DSP Abdullahi, ya ce rundunar ta janye izinin da ta ba jama’a da kungiyoyi da jam’iyyun siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu da sauransu.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa umurnin baya rasa nasaba da tashin hankalin da aka samu biyo bayan takardar neman ba’asi da aka aike wa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan zargin almubazaranci da naira biliyan 3 da milliyan 4 na masarautar karkashin jagorancin sa.
Ya ce akwai bukatar daukar wannan mataki domin gujewa saba doka da oda ta fuskacin tsaro a jihar, inda ya yi gargadin cewa idan aka kama wani mutum ko kungiya da suka tara jama’a ba bisa ka’ida ba , za su fuskacin hukunci.
You must log in to post a comment.