Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta wallafa a shafinta na intanet, cewar maza sun fi mata yawa da kimanin kashi daya a cikin dari. Kasancewar maza na da kashi 50.8, su kuma mata suna da kashi 49.2 a cikin dari na yawan ‘Yan Nijeriya.
Hukumar ta bayyana cewa duk da kokarin da ake yi wurin kara bude wa mata kofar shiga a dama da su a siyasa da mukamai, adadin shigarsu bai wuce kashi 5.8 a cikin dari ba a Nijeriya.
A bangaren wadanda suka fi tsawon rai a tsakanin maza da mata a Nijeriya kuwa, rahoton NBS ya nunar da cewa a shekarar 2016, maza ba su cika wuce shekara 47 a duniya ba, inda mata suka fi su tsawon rai wadanda suke kaiwa shekarar 51 a duniya. A sashen ilimi kuma, adadin ‘yan mata
Yawan tsofaffin da suka haura shekara 60 da haihuwa a Nijeriya kuwa maza suna da milyan 5.54, su kuma mata suna da milyan 4.39.
Hukumar na wallafa rahoton kididdigar yawan mata da maza ne a duk shekara bisa bukatar hakan da aka gabatar a tsarin bunkasa dorewar ci gaba da aka tabbatar a Bejing, babban birnin Kasar Sin.
Bayanan kididdigar an samu ne daga irin bayanan da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ta jihohi suka gabatar a kan sassan tattalin arziki, yawan jama’a, kiwon lafiya, ilimi, ayyuka, karfin iko da kuma yanayin cin zarafin mata.