Hukumomin tsaro a Najeriya sun yi wa harabar gidan talabijin na AIT kawanya bayan an sake bude tashar, bayan rufe ta da hukumar kula da tashohin yada labarai ta Najeriya NBC ta yi na tsawon sa’o’i 24.
Wata kotun tarayya da ke Abuja ce ta soke dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi wa tashar, sannan ta bukaci ta koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
Manajan daraktan tashar, Tony Akiotu, ya ce jim kadan bayan ta fara auki, hukumomin tsaro suka yi kawanya a harabar tashar.
jami’an tsaron sun hada da SSS da kuma DSS na kewaye da tashar ta AIT, sai dai zuwa yanzun ba a fitar da wata sanarwa ba akan dalilinda suka sa jami’an tsaron su ka yi haka.