Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 65 da suka kamu da cutar korona ranar Laraba.
Kazalika, cutar ta kashe ƙarin mutum takwas, a ranar larabar abin da ya kai jumillar adadin wadanda suka mutu zuwa dubu 2 da 922.
Jihohin da aka samu Karin wadanda suka kamun su ne Plateau (22), Abuja (21), Rivers (12), Bauchi (4), Lagos (2), Bayelsa (1), Edo (1), Jigawa (1), Kaduna (1)
Hukumar tace ya zuwa yanzu jumillar mutum dubu 212 da 894 ne aka tabbatar sun harbu da cutar a Najeriya, Sai kuma dubu 204 da 335 da aka sallama daga asibit bayan sun warke.