Home Labaru Rikicin Libiya: An Kashe Hafsoshin Soji 28 A Harin Sama

Rikicin Libiya: An Kashe Hafsoshin Soji 28 A Harin Sama

529
0
Rikicin Libiya: An Kshe Hafsoshin Soji 28 A Harin Sama
Rikicin Libiya: An Kshe Hafsoshin Soji 28 A Harin Sama

Hafsoshin soji akalla 28 ne su ka mutu, a wani harin sama da aka kai wa kwalejin horar da kananan hafsojin soji a birnin Tripoli na kasar Libya.

Duk da yak e ba a samu cikakken bayani game da harin ba, amma rahotanni daga kasar na cewa mayakan Janar Khalifa Haftar da ke yakar gwamnatin kasar ne su ka kai harin.

Rahotanni na cewa, an ga sassan jikkunan mutane da su ka dagargaje a warwatse a cikin wasu hotuna da aka wallafa da ke nuna irin barnar da harin ya yi.

Kakanin ma’aikatar lafiya ta kasar Amin al-Hashemi ya tabbatar da mutuwar kananan hafsoshin soji 28 a harin, wanda ya raunata wasu gommai a kwalejin kananan hafsoshin.

Gwamnatin kasar Libya wadda Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya dai ta dade ta na yakar ‘yan tawayen da janar Khalifa Haftar ke jagoranta.

Rikici da rubawar kai sun barke a kasar ne a shekarar 2011 bayan kashe shugaban kasar da ya dade yana mulki Muammar Gaddafi, bayan hambarar da mulkinsa a lokacin.