Home Labaru Buhari Ba Shi Da Ikon Ya Tirsasa A Rage Ko A Kara...

Buhari Ba Shi Da Ikon Ya Tirsasa A Rage Ko A Kara Kudin Lantarki – Adesina

426
0
Buhari Ba Shi Da Ikon Ya Tirsasa A Rage Ko A Kara Kudin Lantarki - Adesina
Buhari Ba Shi Da Ikon Ya Tirsasa A Rage Ko A Kara Kudin Lantarki - Adesina

Fadar Shugaban Kasa ta ce, Shugaba Muhammadu Buhari ba ya da ikon ya tirsasa ko bada shawarar a kara ko a rage kudin wutar lantarki.

Mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana haka, inda ya ce batun karin kudin wutar lantarki, magana ce daga Ma’aikatar Inganta Makamashi da Hukumar kula da wutar lantar, wadda ke da hakkin kara kudin wuta da kayyade su ba daga tunanin shugaba Buhari ba.

Karin kudin wutar lantarki da aka yi dai ya haifar da guna-guni a tsakanin jama’a, musamman karya kumallon da su ke korafi cewa an yi da karin a farkon shiga shekara ta 2020.

A nata bangaren, hukumar kayyade hasken lantarki ta kasa NERC, ta ce karin ba zai fara amfani ba har sai farkon watan Afrilu mai zuwa.