Home Labaru Harin Ta’addanci: Adadin Sojin Burkina Faso Da Suka Mutu Ya Karu Zuwa...

Harin Ta’addanci: Adadin Sojin Burkina Faso Da Suka Mutu Ya Karu Zuwa 24

480
0

Rundunar Sojin Burkina Faso ta sanar da cewa adadin sojin kasar da aka rasa yayin harin ta’addanci da wasu ‘yan bindiga suka kai musu ranar Litinin na makon nan ya karu zuwa 24.

Harin wanda aka dora alhakin sa kan mayakan da ke ikirarin jihadi a yankin Sahel, ya faru ne a yankin Koutoubou, dake Arewacin gunduman Soum, na Burkina Faso, lokacin da mayakan suka musu kwanton bauna.

A cewar rundunar sojin kasar, baya ga sojin 24 da suka aka rasa akwai kuma wasu soji 7 da yanzu haka ke jinya, yayin da wasu karin biyar kuma suka yi batar dabo bayan farmakin.