Home Labaru Rikicin Jukun Da Tiv: Buhari Ya Bukaci Masu Ruwa Da Tsaki Su...

Rikicin Jukun Da Tiv: Buhari Ya Bukaci Masu Ruwa Da Tsaki Su Lalubo Mafita

348
0
Rikicin Jukun Da Tiv
Rikicin Jukun Da Tiv

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummomin jihar Benue su kwantar da hankulansu biyo bayan kasan Revrend Father David Tanko, a kauyen Kpankufu, Wukari dake jihar Taraba.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya bukaci hakan ne ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu a Abuja.

Sannan Ya bukaci gwamnonin Benue da Taraba da masu ruwa da tsaki su yi ganawar gaggawa domin kawo karshen wannan hatsaniya da ke yiwa jihohin barazana.

Ya ce masu ruwa da tsaki musamman sarakunan gargajiya irin su Tor Tiv da Aku Uka Wukari da malaman addini za su taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da hankula a jihohin.

Sannan ya nuna damuwa bisa yadda ake samun kashe kashe babu gaira babu dalili, inda ya ce gwamnatinsa za ta dau matakan da suka kamata wajen magance matsalar.