Home Labaru Kamfanin NNPC Ya Nemi Hadin Gwiwar Kungiyoyin NUPENG Da PENGASSAN

Kamfanin NNPC Ya Nemi Hadin Gwiwar Kungiyoyin NUPENG Da PENGASSAN

194
0

Babban manajan kamfanin matatar man fetur na kasa Mele Kyari, ya bukaci kungiyoyin ma’aikatan kamfanin su mara masa baya wajen inganta ayyuka.

Ya ce kungiyoyin da suka hada da kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas PENGASSAN da kungiyar ma’aikata ta NUPENG na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen ciyar da bangaren man fetur gaba.

Kyari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai Magana da yawun kamfanin Ndu Ughamadu a Abuja.

Ughamadu ya ce Kyari ya furta hakan ne a lokacin da shugabannin kungiyoyin biyu suka ziyarci shelkwatar kamfanin na NNPC dake Abuja.

Ya ce kamfanin na neman goyon bayan bangarori da dama wajen inganta harkokinsa ta yadda bangaren tattalin arziki zai inganta a Najeriya.

Kyari ya kara da cewa kamfanin zai ci gaba ne kawai idan aka samu masu ruwa da tsaki suka hada hannu tare da magance matsalolin da ke ci masa tuwo a kwarya.