Mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan harkokin tsaro ya ce Iran ta yi babban kuskure wajen kakkabo jirgin amurka.
Donald Trump ya tabbatarwa manema labarai cewa, ba karamin kuskure Iran ta tafka ba wajen kakabo jirgin ta mai sarrafa kan sa, inda ya kara da cewa, za su dauki mataki mai karfi kan lamarin.
Wannan martani na zuwa ne, a dai-dai lokacin da fadar shugaban Amurkar ta bayyana cewa, mai ba Trump shawara a kan harkokin tsaro John Bolton zai tafi Israila, domin tattauna matsalolin da suka shafi tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya tare da wakilan kasashen Rasha da Israila.
Ita kuwa kasar Iran cewa ta yi, zata je Majalisar Dinkin Duniya domin gabatar da shaidar da ke nuna cewa, jirgin da ta harbo ya shiga cikin sararin samaniyar ta.
Ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif ya ce, za su gabatarwa da Majalisar wanan barazana, da ke nuna yadda Amurka ke karya domin tinzira yaki a yankin.
Kungiyar kasashen Turai ta bukaci a yi taka tsan-tsan a kan lamarin, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tura wakili na musamman Iran domin rage takun tsakar da ake samu tsakanin kasar da Amurka.
You must log in to post a comment.