Home Labaru Yaki Da Rashawa: Buhari Ya Sake Sa Hannu Akan Wata Doka

Yaki Da Rashawa: Buhari Ya Sake Sa Hannu Akan Wata Doka

432
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu kan dokar hadin gwiwa wurin yaki masu laifi domin inganta yaki da rashawa a Najeriya da kasashen ketare.

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan ayyukan majalisar tarayya Ita Enang, ne ya bayyana a haka a Abuja, inda ya ce an kafa sabuwar dokar ce domin Najeriya da kasahen duniya su rika taimakawa juna wurin kama masu laifi.

Ya ce wasu daga cikin dalilan da yasa aka kafa dokar sun hada da binciko kayayyaki da kadarorin da masu laifi suka sace da kuma kwato kayayyakin sata da wasu laifuka.

Ita Enang, ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar 20 ga watan Yunin 2019.

Attorney Janar na Najeriya ne ke da wuka da nama wurin karbar bayyanai daga wasu kasashe da kuma neman alfarma wurin kasashen kan duk wani abu da ya shafi wannan dokar.