Home Labaru Ib’tila’i: Gobara Ta Kone Rumfa 25 A Kasuwar Jihar Gombe

Ib’tila’i: Gobara Ta Kone Rumfa 25 A Kasuwar Jihar Gombe

955
0

Wata gobara ta kone rumfuna kimanin 25 a babbar kasuwar jihar Gombe.

Wani shaida gani da idon ya bayyana cewa, wutar ta fara ci ne tun da misali karfe 1:45 na dare, sannan ta shafe tsawon sa’o’i hudu tana ci, wanda hakan ya yi sanadiyar kone rumfuna 25 a kasuwar.

Yayin da ya ke jawabi ga manema labarai, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Alhaji Uba Abdullahi ya ce, wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar, sannan kuma ya ce an yi asarar akalla dukiya da ta kai ta kimanin naira miliyan 50.

Abdullahi ya kara da cewa, wadanda ibtila’in ta shafa sun hada da teloli da masu sana’ar kayan robobi da masu cinikin fata da dai sauran su. Sakataran ma’aikatar kasuwanci na jihar Alhaji Muhammad Malala ya ziyarci kasuwar tare da jajantawa wadanda lamarin ya shafa,  sannan ya yi alkawarin sanar da gwamnati domin ganin ta dauki matakin da ya dace a kan faruwar lamarin.