Home Labaru Rikicin Gabas Ta Tsakkiya: Amurka Ta Aike Da Karin Dubban Sojoji Saboda...

Rikicin Gabas Ta Tsakkiya: Amurka Ta Aike Da Karin Dubban Sojoji Saboda Barazanar Iran

1040
0
Rikicin Gabas Ta Tsakkiya: Amurka Ta Aike Da Karin Dubban Sojoji Saboda Barazanar Iran
Rikicin Gabas Ta Tsakkiya: Amurka Ta Aike Da Karin Dubban Sojoji Saboda Barazanar Iran

Ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar da aikewa da karin dubban sojojin Amurka domin kara karfin kariya ga kasar Saudiyya.

Sakataren Tsaron Amurkar, Mark Esper ya ce, ya amince da aikewa da karin dakaru da suka hada da jiragen yaki da kuma na’u’rorin kariya.

Ya ce hakan martani ne ga irin barazanar da yankin ke fuskanta, a dai-dai lokacin da ake rubanya kokarin kare masarautar daga hare-haren kasar Iran.

Yanzu haka dai, Amurka ta kara dakaru 14,000 a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda gidan talbijin na CNN ya rawaito.

Tun lokacin da aka kai wa matatun man Saudiyya hari da jirgi mara matuki, ake ta zargin kasar Iran da hannua harin.

Shugabannin kasashen France da Jamus da Burtaniya sun ce, babu wata kwakkwarar sheda cewa Iran ce ta kai harin.