Home Labaru Martani: Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Rahoton Cewa An Kai Wa Tawagar Matawalle...

Martani: Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Rahoton Cewa An Kai Wa Tawagar Matawalle Hari

372
0

Gwamnan jihar Zamfara Dakta Bello Matawalle, ya karyata rahotannin da su ka ce ‘yan bindiga sun bude wa tawagar shi wuta a hanyar sa ta zuwa yi wa jama’ar wani kauye da ke karamar hukumar Gusau jajen rashi da asarar da su ka yi sakamakon harin da ‘yan bindiga.

Matawalle Maradun ya ce, jami’an tsaron sa ne su ka fatattaki ‘yan bindigar a wata mafakar su.

A cewar wani shaidar gani da ido, ‘yan bindigar sun kai harin ne a kan tawagar gwamnan yayin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa kauyen Lilo domin yi wa jama’a jaje da ta’aziyya, kuma ‘yan bindigar sun yi amfani da yawan ababen hawa da ke bin hanyar tare da budewa tawagar gwamnan wuta.

Da ta ke musanta labarin a cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin jihar Zamfara ta ce gwamnan da tawagar jami’an tsaron sa ne su ka kai wa ‘yan bindigar hari sabanin labarin da ke yawo a gari.

Mai Magana da yawun gwamnan Yusuf Idris, ya ce Matawalle ne ya jagoranci tawagar jami’an tsaro wajen kai wa ‘yan bindigar hari a maboyar su.

Leave a Reply