Home Labaru Zanga-Zanga: ’Yan Shi’a Sun Karya Kofar Majalisar Tarayya

Zanga-Zanga: ’Yan Shi’a Sun Karya Kofar Majalisar Tarayya

495
0

Mabiya akidar Shi’a sun karya kofar shiga majalisar tarayya ta farko, inda suka kutsa harabar majalisar a Abuja.

Lamarin ya auku ne a lokacin da ‘yan Shi’an suka je bakin kofar, amma jami’an tsaro suka hana, sannan kuma suka shaida musu cewa ba za su sami damar magana da ko  daya daga cikin ‘yan majalisar ba.

Kalaman jami’an tsaron ya fusata su, inda suka yi kukan-kura, suka karya kofa da tsiya, suka kutsa cikin majalisar.

Amma daga bisani mataimakin shugaban majalisar, Yusuf Lasun, ya rufe zaman majalisar da gaggawa, bayan mabiya Shi’an sun antayo cikin majalisar. Tun a shekara ta 2015, bayan jami’an tsaro sun kama Sheikh Ibrahim El-Zakzaky almajiran sa ke gudanar da zanga-zangar ganin an sake shi domin a duba lafiyar sa.

Leave a Reply