Rahotanni na cewa ‘yan Majalisar Wakilai na shirin yin kaca-
kaca da Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila, bisa zargin
karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe da su ka kai dala miliyan
15 daga ɓangaren zartarwa na gwamnati.
‘Yan majalisar da su ka fusata dai sun yi zargin cewa, Gbajabiamila ya ƙulla yarjejeniya da ɓangaren zartarwa a madadin majalisar, na zartar da hanyoyin da za a bi wajen karɓo bashi daga babban bankin Nijeriya na Naira tiriliyan 22 da biliyan 700, amma sai ya gajarce daga abokan aikin sa wajen raba dala miliyan 15 da aka ba Majalisar don jin daɗin yarjejeniyar.
Rikicin da ake fama da shi dai ya tilasta wa Gbajabiamila ɗage ci-gaba da zaman majalisar, wanda tuni aka shirya ranar Talata domin a samu ƙarin lokaci da kuma kwantar da hankulan membobin da ke cikin rikicin.
Kakakin majalisar ya ɗage zaman majalisar ne bisa fakewa da cewa an bayyana ranar ne bisa kuskure.
A cikin wata sanarwa da Magatakardar Majalisar Yahaya Danzaria ya fitar, ya ce, wannan ya na sanar da ɗaukacin ‘yan majalisar da sauran jama’a cewa majalisar wakilai ba za ta koma zaman ta a ranar Talata 16 ga Mayu kamar yadda aka sanar a baya ba.
You must log in to post a comment.