Home Labaru Ba Na Iya Barci Saboda Matsalar Tsaro Lokacin Da Nake Mulki –...

Ba Na Iya Barci Saboda Matsalar Tsaro Lokacin Da Nake Mulki – Jonathan

1
0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce ba ya iya
barci sakamakon matsalar tsaro da ta addabi Nijeriya a
lokacin da ya ke shugabanci.

Jonathan ya shaida haka ne a Jalingo, lokacin da ya ke kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Jihar Taraba a karkashin gwamna Darius Ishaku ta samar.

Da ya ke jawabi lokacin kaddamar da tagwayen hanyoyi masu nisan kilomita 22 daga Panti Napo zuwa sansanin masu yi wa kasa hidima, Jonathan ya jinjina wa al’ummar jihar Taraba bisa rungumar zaman lafiya da su ka yi.

Goodluck Jonathan, ya kuma yaba wa gwamnan da dan kwangilar da ya kula da aikin bisa gudanar da nagartaccen aiki.

Ya ce lokacin da ya ke shugaban Nijeriya,matsalar tsaro ta sa ko barci ba ya iya yi da daddare, domin wasu lokutan ko ya na coci mai bas hi kariya zai kai ma shi waya ya nuna yadda aka kashe mutane ko aka yi garkuwa da su.