Home Labaru An Kama ‘Yan Kwaya’ 534 A Kano, Kaduna Da Wasu Jihohin Nijeriya

An Kama ‘Yan Kwaya’ 534 A Kano, Kaduna Da Wasu Jihohin Nijeriya

66
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya
NDLEA, ta ce ta kama akalla mutane 534 da ta ke zargin su
na ta’ammali da miyagun kwayoyi a wasu jihohin Nijeriya.

Hukumar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ta kama mutanen da tarin miyagun kwayoyin da su ka hada da hodar Ibilis da tramadol da maganin tari na codeine da tabar wiwi da wasu sabbin miyagun kwayoyi.

NDLEA, ta ce ta kama mutanen ne bayan ta kaddamar da wani shirin musamman na kai samame mai taken ‘Operation Mop Up’, wanda aka kaddamar domin kama masu tu’ammali da miyagun kwayoyi kafin rantsar da sabuwar gwamnati.

Hukumar NDLEA, ta ce jihohin da ke kan gaba wajen kamen sun hada da Legas da Kano da birnin Abuja da Kaduna da Bayelsa da Adamawa da Osun da Benue da kuma Filato.

Leave a Reply