Home Labaru Rikici: Iran Ta Musanta Kai Hari Kan Jiragen Daukar Mai A Mashigin...

Rikici: Iran Ta Musanta Kai Hari Kan Jiragen Daukar Mai A Mashigin Tekun Oman

853
0

Kasar Iran tayi watsi da zargin Amurka cewar ita ta kai hari kan wasu jiragen tankunan daukar mai a mashigin tekun Oman, wanda yanzu haka ya haifar da tankiya.
Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif ya zargi Amurka da gagagwa wajen dora zargin kan Iran ba tare da gabatar da wata shaida da zata tabbatar da hakan ba.
Iran ta kuma bayyana Amurka a matsayin barazana ga zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya baki daya.
Sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce suna shaidar dake tabbatar da zargin da suke yiwa Iran.
Pompeo ya ce sun samu kwararan shaidu kan zargin da suke yiwa Iran bayan tattara bayanan asiri, da kuma nazari kan makamin da aka yi amfani da shi, da irin kwarewar da ake bukata wajen amfani da makamin.
Sakataren harkokin wajen na Amurka ya kara da cewa, binciken da suka yi, ya nuna alaka mai karfi tsakanin harin na baya bayan nan, da kuma ire-irensa da Iran ta kai a cikin ‘yan kwanakin nan.

Leave a Reply