Fadar shugaban kasa ta karyata wasu jerin sunaye da aka dinga yadawa a kafafen sadarwa na Intanet cewa su ne sabbin ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A ranar 29 ga Mayu ne dai aka sake rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wa’adin shugabanci na biyu kuma sama da mako biyu kenan aka shafe ba tare da sanar da sabbin ministocin da za su ja ragamar gwamnatin ba.
A wa’adin mulkin sa na farko, shugaban bai nada ministoci ba sai bayan kusan watanni shida da karbar ragamar mulkin kasar.
Yadda ‘yan kasar suka kwashe tsawon lokaci suna jira Shugaba Buhari ya bayyana ministocin sa a farkon mulkinsa, suna fatan a wannan karon ba zai yi jinkiri ba domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Bayan zaben shugabannin sabuwar majalisa, ana tunanin shugaban ya tura sunayen ministocin sa domin fara tantance su. Sai dai ba a san lokacin da za a dauka ba.