Home Labaru Inganta Gidajen Yari: Jamus Za Ta Taimakawa Najeriya

Inganta Gidajen Yari: Jamus Za Ta Taimakawa Najeriya

290
0

Kasar Jamus za ta tallafawa Najeriya wajen gano matsalolin da ke fuskantar gidajen yari, tare da taimakwa wajen canza yadda ake gudanar da su domin a samu nasarar gyara halayen Fursunoni ba tareda karya doka ba.
Rahoton da wasu kungiyoyin kasashen waje da ta ‘Amnesty International’ suka ruwaito akan wani bincike da suka gudanar akan gidaje yarin Najeriya, ya jawo hankalin kasar shirya wani taro na musamman dan kare hakkin bil Adama, da kuma tabbatar da walwalar fursunoni da kuma na jami’an kula da gidajen yarin.
Jami’in gidauniyar da ta shirya taron Vladimir Kreck, ya ce sun lura cewa idan aka duba gidajen yari a kasar Amurka, ko kasashen Turai, za a ga banbancin su da wadan da ke Najeriya, wajen tsafta da kyautata yanayi da yadda ma’aikatan ke kare hakkokin ‘yan jarum.
Kreck, ya ce niyyar gidauniyar shi ne ta kawo masu ruwa da tsaki a rumfa guda, sannan ta taimaka masu ta hanyoyin wayarda kai a hanyoyin zamani da ma’aikatan za su yi amfani da su, wajen cimma burin gyara da warware matsaloli a saukake.
Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasa Ahmed Jafar, ya ce tuni gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bada izinin daukan matakan rage cinkoso a gidajen yari.

Leave a Reply