Wani rahoto da aka fitar kan ‘yan gudun hijira, ya nuna cewa akwai mutane miliyan 41 da ke gudun hijira a fadin duniya.
Rahoton ya bayyana cewa, ‘yan gudun hijira miliyan daya da dubu 200 daga cikin miliyan 41 daga Nijeriya su ka fito.
Haka kuma, rahoton ya ce rikice-rikice da ake yi a nahiyar Afirka sun bada gudummawa wajen karuwar yawan mutanen, yayin da
masifofi daban-daban da aka yi fama da su a fadin duniya su ka tirsasa wa mutane miliyan 28 barin gidajen su zuwa wasu sassan duniya.