Home Labaru Kiwon Lafiya Gyara Dabi’u: An Ceto Kusan Yara 900 Daga Hannun Mayaka A N-Jeriya...

Gyara Dabi’u: An Ceto Kusan Yara 900 Daga Hannun Mayaka A N-Jeriya – UNICEF

298
0

Kimanin kananan yara 900 ne kungiyar sa-kai ta saki bayan ceto su a garin Maiduguri da ke jihar Borno.

Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yaran da aka ceto ana amfani da su ne a wajen aikata miyagun laifuffuka.

UNICEF, ta ce yaran sun shaida yadda ake rikici da kashe-kashen da su ka yi tasiri ga lafiyar kwakwalwa da kuma mu’amalar su.

Bincike ya nuna cwa, akwai sama da mata 100 daga cikin yara 994 da aka saki, wadanda aka kaddamar da shirin gyara masu dabi’u ko hali domin sake komawa kamar sauran mutane.

UNICEF, ta ce tun daga lokacin da su ke samun hadin-kan kungiyar, sama da yara dubu 1 da 700 aka saki, kuma an samu saukin yadda mayakan ke shigar da kananan yara kungiyar su.