Home Labaru Masarautar Kano: An Ba Aminu Ado Bayero Sarautar Bichi

Masarautar Kano: An Ba Aminu Ado Bayero Sarautar Bichi

1740
0

Wasu majiyoyi daga gidan sarautar Kano da kuma gwamnatin jihar, sun tabbatar wa manema labarai cewa Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ba Aminu Ado Bayero sarautar daya daga cikin sababbin masarautun da aka kirkiro a jihar Kano.

An dai bai dan marigayi Sarki Ado Beyeron sarautar Bichi ne a ranar Juma’ar nan.

Wani na kusa da sabon sarkin da ya bukaci a boye sunan sa ya tabbatar wa manema labarai cewa tuni Aminu Bayero ya karbi sarautar.

Mai martaba sabon sarkin Bichin dai shi ne Wamban Kano a yanzu, kuma ya na daya daga cikin manyan ‘ya’yan marigayi Ado Bayero.

Wasu bayanai sun nuna cewa, tuni ‘yan gidan sarautar Kano su ka yi ta kamun kafa wajen gwamna don ganin an nada su sarautar.