Home Home Rasuwar Sarkin Ogbomosho: Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Al’ummar Jihar Oyo

Rasuwar Sarkin Ogbomosho: Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Al’ummar Jihar Oyo

373
0
Rasuwar Sarkin Ogbomosho: Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Al’ummar Jihar Oyo

Rasuwar Sarkin Ogbomosho: Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Al’ummar Jihar Oyo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa jama’ar jihar Oyo da na Ogbomosho kan rasuwar Sarki Jimoh Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III.

A wata sanarwa da babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce mulkin Sarki Oyewumi na shekara 48 ya kawo sauyi matuƙa da kuma zaman lafiya.

Shugaba Buhari, ya jaddada cewa za a ci gaba da tunawa da sarkin kan irin gudunmawar da ya bayar wajen haɗin kan ƙasa musamman a tsakanin sarakunan gargajiya.

Leave a Reply