Home Home Bala’in Guguwa: Shugaba Buhari Ya Jajantawa Gwamnatin Amurka

Bala’in Guguwa: Shugaba Buhari Ya Jajantawa Gwamnatin Amurka

82
0
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Amurka da mutanen ƙasar kan mahaukaciyar guguwar da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi shida.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Amurka da mutanen ƙasar kan mahaukaciyar guguwar da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi shida.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce ya damu ƙwarai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana’o’i da asibitoci suka lalace.

Shugaban kasa ya yi kira ga mutanen Najeriya su taya sauran mutanen duniya addu’a ga waɗanda suka rasa ran su da kuma samun sauƙin wadanda suka jikkata.

Sama da mutum 100 ne suka rasu a guguwar wadda ta fi ɓarna a jihar Kentucky ta Amurka.