Home Home Komawa Ga Allah: Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Fara Alkunutu Kan Kashe-Kashe...

Komawa Ga Allah: Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Fara Alkunutu Kan Kashe-Kashe A Arew

38
0
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar Musulmi su fara gudanar da addu'o'i na alƙunutu game da kashe-kashen da yankin arewa ke fama da shi na 'yan bindiga.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmi su fara gudanar da addu’o’i na alƙunutu game da kashe-kashen da yankin arewa ke fama da shi na ‘yan bindiga.

A cewar wata sanarwar da sakataren JNI Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu, sarkin Musulmin ya nemi dukkan masallatai da majalisun tattaunawa a faɗin Najeriya da su dage da addu’o’i a irin wannan lokaci na bala’o’i domin neman daukin Allah madaukakin sarki.

Mai alfarman ya ce kiran ya zama wajibi idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto, da Gidan Bawa, da Beni-sheikh, da Baga a Jihar Borno.