Home Labaru Rashin Yin Rigakafi Ne Ke Kara Yawaitar Mace-Mace A Najeriya – Dr....

Rashin Yin Rigakafi Ne Ke Kara Yawaitar Mace-Mace A Najeriya – Dr. Faisal

69
0

Gwamnatin tarayya ta ce tana da shaidun da ke nuna cewa sama da kashi 80 cikin 100 na mace-macen da ake samu sakamakon cutar COVID-19 rashin rigakafi ne ke haifar das u.

Shugaban Hukumar Lafiya matakin farko Dakta Faisal Shua’ib ne ya bayyana hakan a wurin taron wayar da kan shugabannin kungiyar daliban Najeriya ta kasa.

Faisal ya ce shaidun da ke gaban hukumar sun nuna cewa yawancin wadanda suka mutu basu yi rigakafin ba.

Ya kara da cewa Rigakafin COVID-19 da ake yi a kasar nan sun tabbatar da ingancinsu, kuma acewarsa an yiwa ‘yan Najeriya miliyan shida allurar rigakafi ba tare da wata illa ba.

Har ila yau ya kuma karyata dukkan zarge-zargen da ake yi na cewa duk wanda aka yi ma allurar rigakafin zai mutu.

A nasa jawabin shugaban kungiyar ta NANS Sunday Dayo ya ce bayan tattaunawar da shugabanin kungiyar suka yi da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya sun tabbatar da  ingancin allurer rigakafin.