Home Labaru Kasar Rasha Zata Saka Jari A Najeriya

Kasar Rasha Zata Saka Jari A Najeriya

98
0

A kokarin inganta dadaddiyar danganta dake tsakanin Najeriya da kasar Rasha, cibiyar kasuwanci da masana’antu tare da hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan kasuwa da ma’adinai da albarkatun noma a Najeriya sun karbi tawagar takwarorin su daga Rasha.

Ana sa ran wannan dangatakar za ta haifar da da mai ido tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama mussaman cinikayya da raya masana’antu da kuma samar da ayyukan yi.

Jakadan Najeriya a Rasha Farfesa Abdullahi shehu wanda ya jagoranci tawagar yace ”an gudanar da tattaunawa kan harkokin man fetur da iskar gas, da noma mussaman samar da kayan aiki da kuma sarrafa ma’adinai da samar da fasaha da kimiya wajen inganta tsaro.

Anasa jawabin wani mamba a cibiyar inganta harkokin kasuwanci a Najeriya Muhammad Yusuf Lere ya ce wannan babbar dama ce ga dukkan kasashen biyu.

Shima shugaban tawagar kamfanonin kasar ta Rasha Ivan Klevtsov wannan babban dama ce ta tada tsohuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Kwararru da dama sun nuna cewar yunkurin da aka yi a wannan karon da kyakyarwar niyar da ake da shi ana sa ran ba zai kare a taron shan shayi kamar yadda akan yi baya ba.

Leave a Reply