Home Labaru Kotu Ta Ki Bada Belin Sheikh Abduljabbar

Kotu Ta Ki Bada Belin Sheikh Abduljabbar

76
0

Wata Babbar kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu a cikin birnin Kano ta sake hana bayar da belin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Lawyan Abduljabbar Muhammad A Mika’il ne ya gabatar da bukatar gaban mai Shar’ia Ibrahim Sarki Yola gabanin kammala zaman kotun na ranar Alhamis din nan.

Gwamnantin jihar Kano ce dai ta ke karar Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zarginsa batanci ga fiyayyen halitta Annabbi Muhammadu S A W da kuma yunkurin tunzura jama’a ta hanayar kalaman da ka iya tada zaune tsaye.