Home Labaru Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50, Sun Kashe Wasu Huɗu...

Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50, Sun Kashe Wasu Huɗu A Zamfara

97
0
Yan bindiga

‘Yan bindiga sun kashe mutane hudu, tare da yin awon gaba da wasu mutanen 50 a garin Gora Namaye da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya sanar da manema labarai haka a birnin Gusau.

SP Shehu, ya ce maharan sun shiga garin ne da tsakar daren ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka kashe mutane hudu sannan su ka sace mutane 50, amma ya ce an tura jami’an ‘yan sanda na musamman zuwa yankin a halin yanzu.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Yakubu Elkana, ya bada umurnin a fara aikin ceto wadanda aka sace nan take.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ya ce kwamishinan ya bukaci mutanen yankin su kwantar da hankulan su, yayin da rundunar ke aiki da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da doka da oda a garin.