Shugaban Majalisar Dattawa Sanata, Ahmad Lawan ya ce, dole ‘yan Nijeriya su yi taka-tsantsan wajen karbar ‘yan Boko Haram da ke ikirarin sun tuba kuma su na neman gafara.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja, Ahmed Lawan ya ce dole a samar da matakan da za su tabbatar da cewa ‘yan ta’addan ba Tuabr-Muzuru su ka yi ba.
Hedkwatar Tsaro ta kasa dai ta ce, sama da ‘yan ta’adda dubu 1, ciki har da kwamandojin Boko Haram da kwararrun sarrafa Boma-Bomai sun mika wuya ga rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Nijeriya.
Da dama Mutane sun yi Allah-Wadai da matakin gwamnatin tarayya na yafiya da gyara da kuma sake shigar da tubabbun ‘yan ta’addan cikin al’umma.
Shugaban majalisar dattawa, ya ce Nijeriya ta na bukatar manufa mai tasiri game da yadda za a tunkari masu aikata laifuffuka da su ka tuba, ya na mai cewa akwai bukatar tantance wadanda su ka yi tubar gaskiya da wadanda su ka mika wuya kawai saboda wasu dalilai.
You must log in to post a comment.