Home Labaru Binciken Mdd: Tababa Kan Shirin Sake Tsugunar Da ‘Yan Boko Haram Da...

Binciken Mdd: Tababa Kan Shirin Sake Tsugunar Da ‘Yan Boko Haram Da Su Ka Tuba

78
0
NIGERIA-BOKO-HARAM-SURRENDERS

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi nuni da cewa, gwamnati na yin wani shiri cikin sirri domin fitar da kwamandojin kungiyoyin ‘yan ta’adda daga dazuzzuka ta re gyara su a kuma sama masu sabbin hanyoyin rayuwa.

Hakan dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da hukumomin tattara bayanan sirri su ka fara gudanar da bincike akan tubar da wasu ‘yan ta’adda sama da dubu 1 da 200 su ka yi makonni uku da su ka gabata.

Binciken dai kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, ya na neman tabbatar da gaskiyar tubar da ‘yan ta’addan su ka yi, ko kuma dabara ce ta kara tsananta ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

Idan dai za a iya tunawa, wasu shugabanni da al’ummomin yankunan Arewa maso gabas da sarakunan gargajiya, sun nuna rashin amincewa da sake shigar da tubabbun ‘yan Boko Haram a cikin al’umma.