Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da
garkuwa da wasu mutum takwas a garin Gwaram dake karamar
hukumar Talatan Mafara na jihar Zamfara.
Mayakan sun far wa kauyen ne akan Babura, sannan suka rika
bi gida-gida suna sace mazauna garin.
Mai magana da yawun rudunar ‘yan sandan jihar Shehu
Mohammed ya ce wadanda aka sace harda matar hakimin garin
da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na gudunmar, Musa
Makeri.
Ya ce ‘yan bindigan sun harbe hakimin bayan ya ki bari su yi
garkuwa da shi , da kuma fadin cewa ya gwammaci a kashe shi a
garinsa akan a kai shi jeji.