Home Labaru Yarjejeniyar Nukiliya: Gwamnatin Biden Za Ta Yi Ganawar Gaggawa Da Iran

Yarjejeniyar Nukiliya: Gwamnatin Biden Za Ta Yi Ganawar Gaggawa Da Iran

255
0

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden zai bukaci
tattaunawar gaggawa da kasar Iran da zarar kasar sa ta koma
cikin yarjejeniyar nukiliyar da ta fice a karkashin mulkin
shugaba Donald Trump.

Biden ya shaida wa Jaridar New York Times cewar, batun na da
tsauri, amma da zarar Iran ta koma mutunta yarjejeniyar da aka
kulla, Amurka za ta koma cikin ta kafin fara tattaunawa.

Jaridar ta ce, gwamnatin Biden za ta kara wa’adin takaita tace
sinadarin Uranium da Iran ke yi domin samar da makamin
nukiliya.

Shugaban ya kuma ce ya zama wajibi Iran ta daina amfani da
kawayenta wajen tada hankali a kasashen Lebanon da Iraqi da
Syria da kuma Yemen tare da Saudi Arabia.

Yayin yakin neman zaben sa, Biden ya yi alkawarin ba Iran
kofar diflomasiyya domin mutunta yarjejeniyar da aka kulla da
ita.

Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da
Kungiyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka kulla
yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2015 wadda za ta hana ta
mallakar makamin nukiliya.

Leave a Reply