Home Labaru Rashin Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Sa Ga Kwamitin...

Rashin Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Sa Ga Kwamitin Zamfara

318
0

Shugaban kwamitin samar da mafita kan matsalolin rashin tsaro a jihar Zamfara Muhammad Dahiru Abubakar, ya ce mutane 500 ne da masu garkuwa da mutgane suka yi garkuwa da su a jihar aka amso su ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.

Da yake  bayani kan ayyukan kwamitin ga manema labarai, bayan wata ziyarar bangirma da suka kai wa mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, a Sakkwato, ya ce wata biyu kacal da kafa kwamitin amman ya fara haifar da da mai Ido

Acewar sa sun je fadar mai alfarman ne domin neman albarka da kuma neman shawarwari a matsayin sa na tsohon soja kuma kwararre kan harkokin tsaro.

Muhammad Dahiru Abubakar, wanda shima tsohon  sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya ne, yace sun zagaya masarautu 16 zuwa 18 dake jihar Zamfara domin neman irin wanan goyon baya kuma sun samu.

A nasa bangaren mai alfarma sarkin musulmin Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi alkawarin amfanin da sauran masarautun yankin Arewa wajen goyon bayan yakin da ake da ayyukan ta’add anci a yakin Arewa baki daya.