Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, ya ce kwararar Fulani zuwa Nijeriya daga kasashen waje ne ke janyo rashin tsaro a fadin kasar nan.
Ortom ya bayyana haka a Makurdi, yayin da ya karbi bakuncin wakilan shugabannin gargajiya daga jihar Nasarawa.
Kamar yadda ya ke kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan Nathaniel Ikyur ya fitar, ya ce sarkin Keffi Shehu Chindo ne ya jagoranci tawagar shugabannin.
Shugabannin gargajiyar dai sun kai wa gwamnatin jihar Benue ziyara ne, domin jajenta masu a kan balaguron farauta da shugaban yankin Idoma Elias Ikoyi Obekpa ya yi.
Samuel Ortom, ya ce kabilun Tibi da Fulani da sauran ‘yan Nijeriya, sun zauna tare cikin zaman lafiya kafin Fulani daga kasar waje su fara shigowa Nijeriya ba tare da an duba su ba.
Ya ce shigar su cikin kasa ba tare da an bincike su ba ne sanadin matsalolin tsaron da Nijeriya ke fuskanta.