Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnan Anambra Ya Sanya Wa Dokar Hana Kiwo A Fili Hannu

Gwamnan Anambra Ya Sanya Wa Dokar Hana Kiwo A Fili Hannu

11
0

Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano ya bi sahun takwarorin sa na yankin wajen sanya hannu a kan dokar hana kiwo a fili.

Willie Obiano, ya ce sun ɗauki matakin kafa dokar ne domin kyautata zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a jihar Anambra.

Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar ta ba jami’an tsaro umarnin fara aiwatar da dokar nan take.

Anambra dai ita ce jiha ta baya-bayan nan da ta kafa dokar, bayan jihohin Rivers da Ondo da Legas da Akwa Ibom da wasu jihohin yankin kudancin Nijeriya.