Home Labaru Takaddama: Kotu Ta Bukaci Ganin Kakakin Majalisar Jihar Kano Da Wasu Mutane...

Takaddama: Kotu Ta Bukaci Ganin Kakakin Majalisar Jihar Kano Da Wasu Mutane 5

5
0
Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano, ta bukaci kakakin majalisar jihar da wasu mutane biyar su bayyana a gaban ta.

Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano, ta bukaci kakakin majalisar jihar da wasu mutane biyar su bayyana a gaban ta.

Umarnin dai, ya biyo bayan korafin da dakataccen shugaban hukumar sauraren korafe-korafen jama’a da yaki da rashawa na jihar Kano Muhyi Rimin-Gado ya shigar.

Sauran wadanda ya ke kara kuma sun hada da Antoni janar na jihar Kano, da babban akawun jihar da kwamishinan ‘yan sanda na jihar da kuma shugaban ‘yan sandan Nijeriya.

Alkalin kotun mai shari’a Jane Iyang, ya bukaci mutanen su bayyana a gaban kotun cikin kwanaki biyar, kuma kada kotun ta amince da duk wata bukatar su.

Ya ce ana bukatar ganin duk wadanda ake karar a cikin kwanaki biyar, sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba domin saurare.