Home Labaru Matsalar Rashin Tsaro: An Sace Kanwar Mataimakin Shugaban Majalisa A Katsina

Matsalar Rashin Tsaro: An Sace Kanwar Mataimakin Shugaban Majalisa A Katsina

46
0
'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki kauyen Tafoki a Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da kanwar mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Katsina, Shehu Dalhatu Tafoki.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga manema labarai, Dalhatu Tafoki, ya ce kanwar tasa da aka yi garkuwa da ita ’yar makarantar sakandare ce kuma an kusa daura aurenta.

Mataimakin shugaban majalisar ya bayyana cewa Sun farmaki kauyen da misalin karfe 1 na dare inda suka wuce kai tsaye zuwa gidan mai gari, wanda shi ne gidan iyayen nasa sannan suka sace kannen mata biyu.