Dakataccen shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen, ya ce wasu daga cikin kudaden da aka tura a asusun ajiyar sa na banki a shekara ta 2015, gudunmuwar bikin auren ‘yarsa ne ba toshiyar baki kamar yadda hukumar EFCC ta yi ikirari ba.
A cikin karar da ta shigar a gaban Majalisar Koli ta shari’a, EFCC ta yi ikirarin cewa an tura wa Onnoghen wasu kudade a cikin asusun ajiyar sa a shekara ta 2015, wadanda su ka ce toshiyar baki ce bisa wasu shari’u da ake yi a kotun koli a lokacin Onnoghen ya na shugaban kotun.
Sai dai a wasikar da lauya mai kare wanda ake zargi ya aike wa wasu manyan alkalai ciki har da tawagar lauyoyin hukumar EFCC, Onnoghen ya musanta zargin da aka yi a kansa, inda ya ce kudin gudunmawar aure ne kamar yadda aka saba yi a al’adar su.Lauya mai kare Onnoghen ya cigaba da cewa, wannan ba laifi ba ne kamar yadda sashe na 13.5 (2) na dokar aikin alkalai na shekara ta 2006 ya nuna, saboda haka al’adar mutanen su ta ke, kuma kudaden ba su da wata alaka da aikin sa a matsayin alkali.